<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><lyrics>[V1]
 1) Ya Yesu Ubangijina
 Ba kome cikin hannuna,
 Ba hujja domin laifina,
 Mai biyan fansa, na zo, na zo.

[V2]
 2) Alkawarinka na ke bi.
 Ba ka korar mai zunubi,
 Mai tuba za ka karƃe shi,
 Mai biyan fansa, na zo, na zo.

[V3]
 3) Dube ni marar ƙarfi fa.
 Ka biya bukatar ruhuna.
 Addu'ar kowa ba ka ƙi,
 Mai biyan fansa na zo, na zo.

[V4]
 4) Ba ni da kome ban da kai,
 Ko kyau ko gaskiya ko rai,
 Kai ne Mai Ceto, kai kaɗai,
 Mai biyan fansa, na zo, na zo.

[V5]
 5) Ƙaunarka marar iyaka,
 Ta sa ni cikin hanyarka,
 Ni bawanka har abada,
 Mai biyan fansa, na zo, na zo.</lyrics>
<title>Ya Yesu Ubangijina Ba Kome Cikin Hannuna LW169</title>
<hymn_number>169</hymn_number>
</song>